Mark 7

Mai Tsabta da Marar Tsabta

1Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa “marasa tsabta,” wato, da ba a wanke ba. 3(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda alʼadun dattawa suka ce. 4Saʼad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu alʼadu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko farko suna da tuluna, butoci da tabarmai.
)

5Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin alʼadun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa ‘marasa tsabta’?”

6Ya amsa, ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa:

“ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,
amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7A banza suke mini sujada,
koyarwarsu dokokin mutane ne kawai.’
Ish 29.13

8Kun bar umarnan Allah, kuna bin alʼadun mutane.”

9Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye alʼadunku! 10Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ 
Fit 20.12; M Sh 5.16
kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’
Fit 21.17; L Fir 20.9
11Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12ta haka ba kwa ƙara barinsa yǎ yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin alʼadun da kuke miƙa wa ʼyaʼyanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”

14Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa, ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko farko suna da ‘marar tsabat.’ 16Duk mai kunnuwan ji, yǎ ji.


16
This verse is empty in this translation.
17Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi maʼanar wannan misali. 18Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, saʼan nan kuma yǎ fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)

20Ya ci gaba: “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ‘ƙazantar’ da shi. 21Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen shaʼawa, kishi, ɓata suna, girmankai da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ‘ƙazantar’ da mutum.”

Bangaskiyar Baheleniya

24Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yǎ sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. 25Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. 26Macen kuwa Baheleniya ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yǎ fitar da aljani da yake jikin diyarta.

27Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ʼyaʼya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”

28Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci ɓurɓudin da suke fāɗuwa daga abincin yaran.”

29Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”

30Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

Warkar da Kurma wanda Yake kuma Bebe

31Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.
Wato, Birane Goma
32A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yǎ ɗibiya hannunsa a kan mutumin.

33Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, saʼan nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”) 35Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

36Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. 37Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”

Copyright information for HauSRK